Bisa sakamakon da hukumar zaben kasar Togo ta bayar, Foure ya samu kuri'u da kashi 58.75 cikin dari, yayin da dan takara na jam'iyyar kawancen neman yin kwaskwarima kan siyasa ta kasar Jean Pierre Fabre ya samu kuri'u da kashi 34.95 cikin dari, haka kuma adadin kuri'un da sauran 'yan takara uku suka samu bai zarce kashi 7 cikin dari ba.
Bisa dokar zaben kasar Togo, idan anana gudanar dajefa kuri'u karo daya kawai zagaye farko a zaben shugabancin kasar, kuma wanda ya fi samun kuri'u ne zai zama shugaban kasar. Ana bukatar daYanzu ana jiran kwamitin tsarin mulkin kasar da ya tabbatar da sakamakon da hukumar zaben kasar ta bayar.
Foure mai shekaru 48 da haihuwa, ya fara zama shugaban kasar Togo ne a karon farko a watan Afrilu na shekarar 2005, sannan ya samu zarcewayi nasarar sake hawan kujerar a karo na biyu a shekarar 2010. (Zainab)