in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dakatar da 'yan wasan kwallon kasar Australia biyu daga buga wasannin
2015-08-13 16:20:45 cri
Rahotanni daga kasar Australia na cewa hukumar shirya wasan kwallon zari-ruga na Australia ko AFL, ta dakatar da 'yan wasan kasar su 2 daga buga wasanni har tsahon shekaru 2, bayan da aka same su da laifin shan wani maganin kara kuzari mai suna clenbuterol.

'yan wasan Josh Thomas, da Lachie Keefe, dake buga wasa a Collingwood Magpies na Australia, sun ce sun amince da hukuncin hukumar ta AFL, bayan da hukumar hana ta'ammali da kwayoyi a wasanni ta yankewa 'yan wasan hukunci.

Shi ma a nasa bangare kulaf din Collingwood, dake matsayin daya daga manyan kulaflikan kwallon zari-ruga a kasar ta Australia, ya bayyana aniyar sa ta fidda 'yan wasan biyu daga jerin masu buga masa wasa.

An dai ce za a fara aiwatar da hukuncin kan 'yan wasan biyu ne daga watan Maris da ya wuce, lokacin da aka fara dakarar da su daga wasanni. Hakan dai na nufin 'yan wasan biyu za su koma buga wasa cikin watan Maris na shekarar 2017.

Clenbuterol dai sinasari ne dake taimakawa nunfashi, kuma tuni hukumar hana shan kwayoyin kara kuzari ta Australia ko WADA, ta hana amfani da shi.

Su dai 'yan wasan biyu sun ce sun sha wannan sinadari ne bisa kuskure, lokacin da suke shan wasu kwayoyi a yayin wani biki cikin watan Fabarairu.

A daya bangaren shugaban kungiyar ta Collingwood Gary Pert, ya ce su da 'yan wasan sun amince da sakamakon da ya biyo bayan gangancin da 'yan wasan suka aikata. Ya ce 'yan wasan biyu sun yi abun kunya, sun kuma bata wayon su, sai dai za su iya tuba, su gyara halayen su bayan aiwatar da hukuncin da aka yanke musu.

An dai dade ana samun matsaloli na shan kwayoyi iri daban daban, tsakanin 'yan wasan kwallon zari-ruga, inda kawo yanzu kulaf din Essendon Football Club ke fuskantar makamancin wannan lamari, bayan da hukumar WADA ta tuhumi 'yan wasan sa a shekarun 2012 da 2013.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China