in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Me za a samu daga wasannin Olympics na lokacin sanyi a shekarar 2022?
2015-08-05 09:40:28 cri

A kwanakin baya, kwamiti mai kula da wasannin Olympics na IOC ya sanar da baiwa birnin Beijing na kasar Sin damar karbar bakuncin gasar Olympics na lokacin sanyi a shekarar 2022, hakan ya sa ake tunanin cewa wace moriya kasar Sin, da jama'arta za su samu daga karbar bakuncin wannan gagarumar gasa?

Wani abu mai burgewa da jami'an gwamnatin birnin Beijing suka ambata, yayin neman karbar bakuncin gasar shi ne burin kasar Sin na "sanya mutane miliyan 300 halartar wasannin na lokacin sanyi". Idan an kwatanta da yawan al'ummar kasar su miliyan 1400, za a gano cewa, burin gwamnatin kasar Sin na nufin sanya kashi 1 cikin kashi 5, na yawan al'ummar kasar fara rungumar wasannin lokacin sanyi, wadanda suka hada da wasan kankara, da wasan zamiya tsakanin duwatsu, da dai makamantansu.

Sa'an nan idan an yi nazari kan mutanen da suke shiga wasanni a lokacin sanyi, za a ga cewa ana iya raba su kashi 2: A bangaren farko akwai kwararrun 'yan wasa, da masu sha'awar wasan kankara, yayin da sauran suke bangaren wadanda ba su da kwarewa a wasan kankara, amma suna da sha'awar su gwada wasu fasahohi na wasan kankara, ko kuma su dandano abin da ake ji a zuciya yayin wasan kankara, gami da sauran wasannin motsa jiki a lokacin sanyi.

Saboda samun ci gaban tattalin arziki, yanzu a nan kasar Sin ana ta samun karin al'ummar kasar da suka fara sha'awar wasannin lokacin sanyi, musamman ma ta la'akari da yadda a wannan karo, Beijing da Zhang Jiakou suka samu damar karbar gagarumar gasar Olympics ta lokacin sanyi, wadda ake ganin cewa za ta janyo hakalin karin jama'ar kasar zuwa ga wasannin lokacin sanyi.

Hakika yanzu a birnin Beijing, idan ka je wuraren wasan kankara wadanda yawancinsu suka kasance a karkarar birnin a lokacin sanyi, za ka ga mutane masu yawa, musamman ma bayan da matasa suka fara hutun su a lokacin hunturu. Hakan ya kasance alamar da ke shaida yadda wasannin kankara suke samun karin karbuwa tsakanin al'ummar kasar Sin.

Ban da wasan zamiya kan allo, da zamiya a takalman kankara wadanda suka kasance wasannin kankara na yau da kullum, wasan kwallon gora a kan kankara wato "Ice-hockey" a Turance, shi ma ya fara farin jini a nan kasar Sin. Wasan da ya hada da fasahar wasan kankara da ta kwallon gora, yana kuma bukatar 'yan wasa da suka samu kwarewa sosai kan wasan kankara, da karfin jiki, da hazaka, don haka shi ma yana janyo hankalin matasa sosai.

Alkaluman da aka samu daga hukumar wasan Ice-hockey ta birnin Beijing sun nuna cewa, 'yan wasan Ice-hockey na birnin su 1000 sun halarci wasanni 420 a kakar wasa ta 2013-2014, yayin da a kakar wasa ta 2014-2015, 'yan wasa fiye da 1900 suka halarci wasanni 759, jimillar da ta ninka ta baya.

Wannan yanayin da ake ciki a nan birnin Beijing na samun karin mutane masu sha'awar wasannin lokacin sanyi, ya taimakawa birnin samun nasara a kokarin neman damar karbar bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi, yayin da a nasa bangare damar da birnin Beijing ya samu, ta sa kaimi ga wasannin lokacin sanyi wadanda ke gama sassan kasar ta Sin.

Mun san cewa kasar Sin sai a arewacinta ne ake samun kankara a lokacin sanyi, yayin da a wasu wuraren kasar dake kudu babu kankara ko kadan, ko da kuwa a lokacin sanyi. Amma hakan bai hana yaduwar wasannin kankara zuwa kudancin kasar ba. A birnin Shanghai, an kafa filayen kankara guda 7, wadanda ko a lokacin zafi ma ana iya amfani da su. Sa'an nan a birnin Nanning, dake kudancin kasar Sin mai nisa, an kafa wani filin kankara, wanda ya taimakawa wata yarinya cimma burinta. Yarinyar mai suna Wu Ruoyun ba ta taba ganin kankara ba kafin shekarar 2013, amma bayan ta yi watanni 3 tana samun horo a fannin wasan kankara, an gayyace ta don ta halartarci gasar wasan kankara ta nahiyar Asiya, wadda ta gudana a birnin Beijing a shekarar 2013.

Duk wani wasa, idan ana so a yayata shi, tilas ne a yi kokarin yayata shi tsakanin matasa, domin su ne manyan gobe, kuma wadanda za su yada fasahohinsu ga karin mutane. Saboda haka, tun daga shekarun 1990, hukumomin kasar Sin masu kula da wasanni sun tsara wasu shirye-shirye na wayar da kan matasa dangane da wasannin kankara, don sanya su sha'awar wasannin. Hakan ma ya kasance wani bangare ga kokarin hukumar kasar na samun damar karbar bakuncin gasar Olympics na lokacin sanyi.

Karkashin yanayin da muke ciki na kokarin share fagen gasar da za ta gudana a shekarar 2022, za a gano habakar filayen wasannin kankara, da kara gina wasu a nan birnin Beijing. Yanzu birnin Beijing yana da irin wadannan filayen sama da 10, duk da cewa yawan al'ummar birnin ya kai fiye da miliyan 20. Amma a birnin Vancouver na kasar Kanada, wanda shi ma ya taba karbar bakuncin gasar Olympics a lokacin sanyi, yawan filayen wasan kankara ya kai fiye da 100, yayin da yawan al'ummar birnin bai wuce dubu 600 ba. Hakan ya shaida wani gibin da birnin Beijing zai yi kokarin cike wa.

Kasar Japan makwabciyar kasar Sin ita ma ta taba karbar bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi sau 2, a biranenta na Sapporo a shekarar 1972, da Nagano a shekarar 1998. Gasar Olympics da ta gudana a Sapporo ta taimakawa kokarin yayata wasannin kankara zuwa sauran kasashen nahiyar Asiya, wadda kuma ta sanya tattalin arzikin kasar Japan, wanda ya lalace matuka sakamakon babban yakin duniya na biyu, farfadowa cikin sauri. Yayin da a nashi bangare, Nagano shi ma ya samu ci gaba sosai a fannin yawon shakatawa da tattalin arziki. Saboda haka, ana sa ran ganin birnin Beijing da na Zhang Jiakou, da kasar Sin baki daya sun samu amfana mai yawa ta hanyar karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin sanyi a shekarar 2022. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China