Rafael da Silva dai shi ne dan wasa na 3 da Lyon ya dauka a bana, bayan Jeremy Morel na Marseille, da kuma Claudio Beauvue na Guingamp. Lyon dai ya dauki kofin kungiyoyi Ligue 1 har karo 7. A kuma wannan karo ya cimma matsaya da Manchester United, domin dakko Rafael dan asalin kasar Brazil.
Sanarwar da kulaf din na Lyon ya fitar ya bayyana cewa tuni Rafael ya gudanar da gwajin lafiya, za kuma a gabatar da shi a karshen makon dake tafe. Rafael dan shekara 25, ya fara taka leda a Manchester United ne a shekara ta 2008, bayan ya bar kulaf din Fluminense na kasar Brazil shi da dan uwansa Fabio, ya kuma buga wasannin 169, tare da lashe manyan gasanni 3 da gasar League daya.
Sai dai a karkashin horaswar Louis van Gaal, Rafael ya rasa damar sa ta taka wasa sosai, sakamakon canjin sa da ake yawan yi. Bisa wannan dama ta sauya sheka da ya yi zuwa Lyon, Rafeal ya ce ya godewa magoya bayan Manchester United bisa kauna da suka nuna masa tsahon shekaru, kamar dai yadda ya rubuta a shafin sa na Twitter, jim kadan da bashi umarnin barin tawagar Man Unt dake buga wasannin share fage a kasar Amurka.(Saminu Alhassan)