Yayin wasan neman matsayi na 3 a gasar wadda hukumar kwallon kafa ta tsakiya da gabashin Afirka Cecafa, da hadin gwiwar shugaban kasar Rwanda Paul Kagame suka dauki nauyin shiryawa, Uganda ta doke takwararta ta Sudan da ci 2 da 1.
Baya ga lambar tagulla da aka mikawa kungiyar ta kasar Uganda, an kuma baiwa kulaf din kyautar kudi har dalar Amurka 10,000.
Da yake bayyana farin cikin sa game da wannan nasara da kulaf din sa ya samu, mukaddashin babban jami'in kungiyar ta KCCA David Tamale, ya ce hakan babbar nasara ce kasancewar sun hada kungiya mai cike da kwararrun 'yan wasa, da kuma sabbin masu horas da 'yan wasa 2.
A wasan karshe da aka buga a karshen makon jiya, kungiyar Azam FC ta Rwanda ce ta lashe kofin, bayan da ta samu nasara kan abokiyar karawar ta wato Gor Mahia FC ta kasar Kenya da ci 2 da nema. Sakamakon hakan kulaf din Rwanda ya samu kyautar kudi har dalar Amurka 30,000, yayin da kulaf na biyu wato kungiyar Kenya, ta karbi kyautar dalar Amurka 20,000.
Kungiyoyi 13 da suka buga wannan gasa dai sun hada da Tanzania, da Kenya, da Djibouti, da Zanzibar, da Sudan.Sai kuma Rwanda, da Burundi, da Somalia, da Sudan ta kudu, da Habasha da kuma kasar Uganda.(Saminu Alhassan)