Shugabannin kasashen kudancin Afrika sun amince da shirin yaki da ta'addanci na shiyya-shiyya a yayin taron kungiyar raga kasashen kudancin nahiyar SADC karo na 35.
Shugabannin kasashe da jami'an gwamnatin na kasashen kungiyar ta SADC mai mambobi 15 suka halarci taron shugabannin kasashe da gwamnatoci na shekara shekara tsakanin ranakun Litinin da Talata na wannan makon a Gabarone, babban birnin kasar Botswana.
Sanarwar bayan taron da aka fitar a ranar Talatan ya ce, yankin na bukatar samun manufa da tsari daya ta yadda za'a kare tare da magance duk wassu nau'in ayyukan ta'addanmci daga gida ko kasashen waje.
Kungiyar SADC na daya daga cikin kungiyoyin da kasashen take zaman lafiya a nahiyar.(Fatimah Jibril)