A gun taron, Sabon shugaban kungiyar a wannan karo kuma shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashe membobin kungiyar su kara yin hadin gwiwa wajen samar da kayayyakin more rayuwa, kana ya yi kira da a gina manyan hanyoyin jiragen kasa a manyan birane da cibiyoyin cinikayya na kasashen don sa kaimi ga samun bunkasuwar masana'antu a nahiyar Afirka.
Taken taron na wannan karo shi ne sa kaimi ga yin amfani da albarkatun da allah ya hore wa yankin da samun bunkasuwa mai dorewa a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, ana fatan gabatar da hadaddiyar sanarwar bayan taro a ranar 18 ga wata. (Zainab)