in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kira taron koli karo na 33 na kungiyar SADC
2013-08-18 16:45:20 cri
Jiya Asabar 17 ga wata, an kaddamar da taron koli karo na 33 na kungiyar raya kudancin kasashen Afirka, wato SADC a birnin Lilongwe, hedkwatar mulkin kasar Malawi. Taron za a shafe kwanaki biyu ana yinsa, inda Joyce Banda, sabuwar shugabar kungiyar SADC kuma shugabar kasar Malawi ta furta cewa, SADC za ta dora muhimmanci kan raya ayyukan gona, da kuma ci gaba da ingiza yunkurin dinkuwar yankin da mambobin kungiyar ke ciki.

An sanya "Tinkarar wata makoma iri daya" a matsayin babban taken taron na shekarar bana. Kuma kasar Malawi ta maye gurbin kasar Mozambique don shugabancin kungiyar SADC a wannan zagaye, kana shugabar kasar Malawi Joyce Banda ta zama sabuwar shugabar kungiyar, wadda ta kasance daya daga cikin shugabanni mata biyu na kasashen Afirka da ke kan karagar mulkin kasa.

Bisa kididdigar da kungiyar SADC ta bayar kafin taron, an ce, a halin yanzu dai, mutane miliyan 14 na kasashe mambobin kungiyar na fama da matsalar karancin abinci, inda rashin samun isasshen hatsi na ci gaba da kawo barazana ga yankin. Don haka, shugaba Banda ta jaddada cewa, ya kamata kungiyar ta dora muhimmanci kan batun raya ayyukan gona domin raya tattalin arziki da kuma kawar da kangin talauci.

A shekara ta 2008, kungiyar ta kaddamar da aikin raya yankin ciniki maras shinge. Haka kuma a yayin taron musamman na zuba jari kan muhimman ayyukan more rayuwar jama'a da ta kira kwanan baya, kungiyar ta tsara wani shirin raya muhimman ayyukan more rayuwar jama'a daga shekara ta 2013 zuwa ta 2017, inda za a kebe kudi Dala biliyan 65 a cikin shekaru biyar masu zuwa domin kaddamar da wannan babban aikin da ya shafi kasashe daban daban, a kokarin gaggauta yunkurin dinkuwar yankin gu daya.

Game da batun, shugaba Banda ta nuna cewa, ya kamata kungiyar ta gaggauta wannan aiki domin tinkarar tabarbarewar tattalin arziki da mummunan yanayin tattalin arziki na waje ke haddasawa. Sakamakon haka, ba kawai ya kamata a sa kaimi ne ga cudanyar cinikayya a tsakanin kasashe mambobin kungiyar ba, kamata ma ya yi a kara azama ga cudanyar mutanen kasashen cikin 'yanci.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China