Taron na kwanaki biyu ya samu halartar shugabannin kasashe membobin kungiyar ta SADC 15 da na kungiyar AU. Sabon shugaban kungiyar a wannan karo kuma shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi nuni cewa, ya kamata a canja yadda ake sayar da albarkatun kasashen yankin cikin araha, da kuma kara sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen dake yankin.
A gun bikin bude taron, Mugabe ya bayyana cewa, allah ya hore wa kasashe membobin kungiyar SADC albarkatun ma'adinai, amma a kan sayar wa kasashen waje cikin araha. Kamata ya yi kasashen yankin su kafa tsarin sha'anin samar da albarkatun ma'adinai, da kuma yin kokarin kara samun sabuwar moriya daga kayayyakin da suka kera da kuma samar da aikin yi ga jama'arsu. (Zainab)