in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin ba da jinya na kasar Sin ya samu lambar yabo mafi girma daga kasar Senegal
2015-08-19 10:05:05 cri

A jiya Talata, an yi bikin ba da lambar yabo mafi girma ga rukunin ba da jinya na 15 da kasar Sin ta tura Senegal a asibitin Pikine dake yankin karkarar Dakar, babban birnin kasar Senegal, an ba da lambar yabo mai dauke da tambarin zaki wato lambar yabo mafi girma ta kasar Senegal ga shugaban rukunin Weng Wei, kana an ba da lambar yabo ta zinariya ga sauran mambobin rukunin.

Shugabar asibitin Pikine Khadidiatou Sarr Kebe ta ba da lambar yabo ga Weng Wei a madadin ministan kiwon lafiya na kasar Senegal, ta yi kuma jawabi domin nuna godiya kan ayyukan da wannan rukunin ba da jinya na kasar Sin ya yi a asibitin Pikine cikin shekaru biyu da suka gabata, ta kuma kara da cewa, likitocin Sin sun ba da gundumawa sosai wajen cigaban asibitin.

Mr. Weng Wei ya ce, tun lokacin da rukunin ba da jinya na 15 na kasar Sin ya isa kasar Senegal a watan Satumba na shekarar 2013, ban da gudanar da ayyukan yau da kullum a asibitin Pikine, wadannan likitocin Sin sun ba da jinya kyauta a kasashen Senegal da Mali, kuma sun ba da magunguna ga fararen hula, kuma sun taka muhimmiyar rawa wajen rigakafi da yaki da cutar Ebola a kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China