Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya bayyana a ranar Litinin a birnin Dakar cewa, shigowar kasar Sin a nahiyar Afrika ba zai kasance ba wani abin tada hankali ga kasashen yammacin duniya, in ji shugaban kasar, ya kamata su amince yin takara tare da kasar Sin a Afrika. Na sani cewa, shigowar kasar Sin na ta da hankalin kasashen yammacin duniya sosai, amma ya kamata su dubi wannan a matsayin alheri, in ji shugaba Macky Sall a yayin dandalin tattalin arziki na kungiyar kasashen dake amfani da harshen Faransanci da aka bude a ranar Litinin a birnin Dakar.
A gaban shugabannin siyasa na kasashen dake amfani da harshen faransanci wato Francophonie, da suka hada da tsohon faraministan kasar Faransa Alain Jupe, masanan tattalin arziki, masu masana'antu da sauransu, shugaban kasar Senegal ya ba da sha'awarar hada karfi da karfe tare tsakanin kasashen yammacin duniya, 'yan Afrika da Sinawa domin fuskantar bukatun Afrika da suka rataya kan zuba jari sosai kuma mai yawa. (Maman Ada)