in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sandar Senegal sun tarwatsa taron gangamin 'yan adawa
2015-02-02 10:49:17 cri

Yan sandar kasar Senegal sun tarwatsa a ranar Asabar wani taron gangamin jam'iyyar adawa ta (FPDR) ta tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade, da ta fito domin yin allawadai da yadda hukumomin kasar ke tafiyar iko a halin yanzu, a cewar wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Taron gangamin da aka tsai da shirya tun daga dandalin Obelisque tare da halartar tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade, wanda ya jagoranci kasar Senegal daga shekarar 2000 zuwa 2012, bai samun amincewa daga magajin garin birnin Dakar ba, bisa dalilin cewa, takardar da masu shirya gangamin suka gabatar ba ta bayyana wurin da jama'ar za su taru ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China