in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru a fannin aikin gona na kasar Sin dake kasar Senegal sun ba da gundummawa wajen yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu
2015-06-10 11:32:15 cri

A kwanan baya, jakadun wasu kasashen Asiya dake kasar Senegal da wakilin hukumar FAO dake kasar da kuma masanan tattalin arziki na bankin duniya dake kasar sun kai ziyarar aiki a wasu gonakin gwaji da aka noma kayan lambu da wasu kwararrun kasar Sin masu fasahar aikin gona suka kafa.

Tun daga watan Oktoba na shekarar 2006, kasar Sin ta fara tura rukunin kwararru a fannin aikin gona zuwa kasar Senegal har sau biyar. Aikin gona muhimmin aiki ne dake da nasaba da tattalin arziki da zaman rayuwar jama'ar kasar Senegal. Amma har yanzu kasar Senegal, wadda ke da kyakkyawan yanayi a fannin raya aikin gona, na fama da karancin shimkafa a sakamakon rashin fasahohi, dalilin haka ne ma kasar take shigo da kashi 60 cikin dari na duk yawan shimkafa da take bukata daga kasashen waje. Tun lokacin da rukunin kwararrun kasar Sin ya isa jihar Podor a shekarar 2006, wadannan kwararru sun ba da horaswa da dama ga manoman wurin, a sakamakon haka, an samu damar kara karfin samar da shimkafa a kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China