Kasar Senegal za ta aike nan da dan lokaci mai zuwa da wata tawagar ministoci a Conakry domin nazarin hanyoyin sake bude iyakokinta na kasa tare da kasar Guinea, da aka rufe dalilin barkewar cutar Ebola, in ji talabajin din kasar Senegal a ranar Litinin.
Wannan matakin, an dauke shi ne a yayin wata ganawa a birnin Dakar tsakanin shugaban kasar Senegal Macky Sall da takwaransa na Guinea Alpha Conde.
Kasar Senegal, bayan wani umurni na kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), za ta sake bude iyakokinta na sama da na ruwa tare da kasashen da suka fi fama da cutar Ebola. (Maman Ada)