Shugaban kasar Senegal Macky Sall da yanzu haka yake ziyarar aiki a kasar Algeriya ya ce, kasashen biyu sun amince su farfado da dangantakar tattalin arziki, musamman ta inganta ka'idojin da za su shafi hakan domin hadin gwiwwar.
Macky Sall ya bayyana hakan ne bayan da ya tattauna da takwaransa Abdelaziz Bouteflika, ya bayyana wa manema labarai cewa, sun jaddada kudurin farfado da dangantakar tattalin arzikin, kasuwanci da zuba jari.
Ya ce, Algeriya da Senegal ba su da wata matsala ko tashin hankali a tsakaninsu ya zuwa yanzu, sannan dangantakar su kawai tana dan bukatar dan inganta ne.
Shugaban kasar ta Senegal a ranar Litinin ne ya fara ziyarar aiki ta kwanaki 4 a kasar Algeriya domin inganta zumunci a tsakanin su da kuma tattauna halin da ake ciki a yankin Sahel na Afrika. (Fatimah)