in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun kwance bama-baman da aka dasa a kan wasu hanyoyi a Najeriya
2015-08-05 20:39:56 cri
Dakarun Najeriya da ke yaki da mayakan Boko Haram a jihohin da ke yankin arewa maso gabashin kasar, sun ce sun yi nasarar kwance wasu bama-babam da aka dasa a kan hanyar Gwoza zuwa Yamteke da 'yan ta'adaddan suka dasa.

Kakakin runduna ta 7 ta sojojin Najeriya Kanar Tukur Gusau wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a garin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno, ya kuma ce dakarun sun yi nasarar gano wasu wuraren da ake kera makamai da sauran abubuwan fashewa.

Kakakin ya kuma nanata kudurin sojojin na tabbatar da cewa, an kawar da mayakan na Boko Haram tare da mai da zaman lafiya a yankin baki daya.

A 'yan kwanakin nan ne kuma dakarun sama da na kasa suka yi nasarar lalata sansanonin mayakan na Boko Haram yayin wani samamen hadin gwiwa da suka kaddamar a shiyyar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China