Jami'in wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya shaidawa wakilinmu cewa, dakarun wata kungiya mai goyon bayan kungiyar Al-Qaeda, da kuma na kungiyar IS ne suka gwabza fada, bisa wani dadadden sabani dake tsakanin su. Jami'in ya kuma kara da cewa, yayin dauki ba dadin, dakaru 3 daga tsagin masu goyon bayan Al-Qaeda sun mutu, yayin da aka harbe mutane 16 daga bangaren kungiyar IS.
Tun dai hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar ta Libya Muammar Gaddafi a shekarar 2011, ake ta fuskantar matsalolin rashin zaman lafiya, musamman ma daga watan Agustan bara zuwa wannan lokaci, inda majalissu 2 da gwamnatoci 2 ke ikirarin gudanar da mulkin kasar, yayin da kuma magoya bayan kungiyar Al-Qaeda da na kungiyar IS ke ci gaba da samun gindin-zama a kasar. (Bako)