in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sudan ta gargadi Libya saboda da baiwa 'yan tawaye mafaka
2015-08-12 11:33:13 cri

Hukumar lura da al'amuran soji ta kasar Sudan ta gayyaci jami'in sojan da ke ofishin jakadancin kasar Libya da ke Khartoum da ya bayyana a gabanta domin bada bahasi kan batun zargin bada mafaka ga dakarun kungiyar mayakan sakai a yankin Darfur.

Rundunar sojin Sudan ta gayyaci jami'in gwamnatin Libya domin ya yi mata cikakken bayani dangane da zargin bada mafaka da kuma tallafi ga kungiyar 'yan tawayen ta Minni Arko Menawi domin su yaki gwamnatin ta Sudan, kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin ta Sudan Al-Sawarmy Khalid Saad ya tabbatar da hakan.

Mista Al-Sawarmy ya kara da cewa, wannan halayyar tamkar barazana ce ga zaman lafiyar kasar Sudan musamman ma yankin na Darfur, da ma kan iyakar kasashen biyu wanda zai iya haifar da karuwar zaman zulumi ga al'ummar kasar sakamakon yiwuwar fuskantar ayyukan 'yan tawayen da tilastawa mutane shiga ayyukan 'yan tawayen da karuwar fashi da makami a sassan kasar.

Kazalika mai magana da yawun sojan kasar ta Sudan ya ce, ba za su amince da wannan yunkuri na gwamnatin Libya ba, kuma za su yi iyakacin kokarinsu domin tabbatar da kare muradun gwamnatin Sudan.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China