Wani jami'in hukumar tsaron ya bayyana cewa, akwai kamfanin samar da wutar lantarki ta hanyar karfin ruwa a madatsar ruwan ta Haditha, kuma yawan wutar lantarki da kamfanin ke iya samarwa ya kai Walt biliyan 1. Don haka lalata madatsar ruwan, zai haifar da illa ga samar da wutar lantarki ga dukkanin kasar ta Iraki, kuma mai yiwuwa ne hakan ya haddasa bala'in ambaliyar ruwa. (Zainab)