Mashawartan 80 na Amurka sun sauka a sansanin sojojin sama na Habbaniyah, wani mamban kwamitin gundumar Anbar Eid Ammash ya fadi hakan a cikin wata hira da 'yan jarida.
Wadannan mashawarata a fannin harkokin soja zasu horar da jami'an tsaro da mayakan kabilu da kuma taimakawa masu da kayayyaki da tsare tsaren soja a yayin yake yake a biranen Ramadi da Falloujah domin karbe su daga hannun kungiyar IS, in ji mista Ammash.
Mista Ammash yayi wadannan kalamai kwanaki uku bayan fadar White House ta sanar da amincewar shugaban kasar Amurka Barack Obama na tura karin ma'aikatan soja 450 a kasar Iraki domin horar, bada shawara da bada taimako ga sojojin Iraki da mayakan kabilun darikar sunni da ke yaki da kungiyar IS.
Kungiyar IS ta karbe yanki mafi girma a gundumar Anbar, yanki mafi girma a Iraki, kuma kungiyar na kokarin shiga birnin Bagdad, amma mai da martanin dakarun gwamnatin kasar Iraki da dakarun sa kai na Shi'a sun tilastawa mayakan IS ja da baya.
Matsala ta fuskar tsaro a Iraki ta kara tabarbarewa sosai tun farkon barkewar munanan tashe tashen hankali a cikin watan Yunin baya tsakanin jami'an tsaron Iraki da mayakan kungiyar IS. (Maman Ada)