Al-Abad ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a gidan telebijin mallakar kasar a daren jiya Laraba.
A daya hannun kuma shugaban kwamitin tsaron majalisar dokokin jihar Salahudin ya bayyanawa 'yan jarida cewa, jiragen saman yaki na kasar Iraki, sun kaddamar da hari kan sansanin dakarun kungiyar IS dake yankin gabashin birnin Tikrit, musamman a gabar kogin Tigris, da kuma wurin dake kewaye da fadar tsohon shugaban kasar Saddam Hussein, bisa taimakon jiragen sama na kawancen kasa da kasa kan yaki da kungiyar IS.
An ce harin ya lalata dakuna da dama da aka ajiye makamai a cikin su, da kuma motocin soja masu dauke da manyan makamai, baya ga mutane da dama, da kuma mayakan kungiyar ta IS wadanda suka rasa rayukan su. (Zainab)