in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sudan ya alkawarta hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin warware rikicin kasa Libiya
2015-05-31 16:57:11 cri
Shugaba Omar Al-Bashir na Sudan, ya bayyana aniyar sa ta hada kai da sassan masu ruwa da tsaki, da nufin kawo karshen rikicin dake addabar kasar Libiya.

Al-Bashir ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da jakadan firaministan kasar Libiyan Nuri Almal, wanda ya gabatar ma sa rubuttacen sako daga firaministan Libiyan Abdullah al-Thani. Sakon da ke kunshe da bayanan irin ci gaba da aka samu, a kokarin warware rikcin siyasar kasar ta Libiya.

Da yake tsokaci game da hakan, shugaba Al-Bashir ya nanata burin ganin an koma teburin shawarwari, tsakanin sassan dake adawa da juna a kasar ta Libiya. Ya ce alakar kasashen biyu na kara inganta a dan tsakanin nan, bayan tsamin da dankantakar ta su ta yi a baya.

A karshen shekarar da ta gabata ma dai Sudan ta kira taron shugabannin kasashe makwaftan Libiya, domin duba yiwuwar shawo kan rikicin kasar. A kuma wannan lokaci ne aka fidda sanarwar bayan taro da ta yi kira ga daukacin bangarorin dake dauke da makamai a Libiyan da su koma zaman tattaunawa

Libiya, wadda ke da tarin arzikin mai a yankin Arewacin nahiyar Afirka, na shan fama da rikicin siyasa tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Muammar Gaddafi a shekarar 2011, inda a yanzu sashen masu ra'ayin baruwan mu, da na masu ra'ayin Islama ke kokawar amshe madafan ikon kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China