Wannan ne karo na farko da MDD ta bayar da lambar yabo ta Nelson Mandela. A cikin jawabin da mista Sam Kutesa, shugaban babban taron MDD karo na 69 ya bayar, ya bayyana cewa, likita Helena Ndume ta yi aikin tiyata kyauta ga 'yan Namibia fiye da dubu 30 wadanda suka kamu ciwon ido. Sannan tsohon shugaba Jorge Fernando Sampaio na kasar Portugal ya taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan cutar Aids da yakar miyagun kwayoyi, da kare hakkin bil Adama da kuma kokarin ilmantar da karin yara a lokacin da yake kan mukamin shugabantar kasarsa. Dukkansu biyu sun bayar da gudummawarsu sosai wajen taimakawa sauran mutane.
Sannan a cikin jawabinsa, mista Ban Ki-moon, babban sakataren MDD ya ce, wadanda suka samu lambar yabo ta Nelson Mandela sun yi kokarin shimfida adalci a zaman al'umma, da taimakawa wadanda suka sha wahala da su tsira daga mawuyacin hali da kuma samun karfi. Sakamakon da suka samu ya samu amincewa. Ruhun Nelson Mandela na sa kaimi ga duk duniya baki daya, ya kamata gamayyar kasa da kasa ta kara yin kokarin kare hakkin bil Adama da neman bunkasuwa da kuma shimfida zaman lafiya domin nuna girmamawa ga marigayi Nelson Mandela.
A watan Yuni na shekarar 2014 a yayin babban taron MDD karo na 68, an zartas da kudurin kafa lambar yabo ta Nelson Mandela domin nuna girmamawa ga marigayi Nelson Mandela da kuma yaba wa wadanda suka bayar da gudummawarsu sosai ga yada ruhu da ka'idodjin MDD. (Sanusi Chen)