Mr. O'Brien ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ofishin sa ya fitar a jiya Laraba, ya ce wadanda za a fi baiwa kulawa a wannan aiki sun hada da miliyoyin mutanen da tashe-tashen hankula suka raba da muhallan su a kasashe irin su Chadi, da Eritrea, da Habasha, da Myanmar, da Somalia da kuma Sudan.
Sanarwar ta kara da cewa an ware dala miliyan 20 domin rabawa kasashen Sudan da Chadi, cikin wannan adadi za a yi amfani da wani kaso wajen samar da hidima, da tsaron rayukan miliyoyin jama'a a yankunan Darfur dake Sudan, wadanda ya zuwa yanzu ke shan fama da rigingimu tsahon kusan shekaru 13.
Kaza lika an ware wa kasashen Eritrea, da Habasha da Somalia dala miliyan 33, kasancewar wadannan kasashen na cike da tasirin sauyin yanayi, yayin da kuma al'ummun su ke fama da yawan tashe-tashen hankula.
O'Brien ya kara da cewa bada tallafin kudade shi ne mataki na karshe, na ceto mutanen da ke fuskantar halin ha'u la'i a sassan duniya daban daban. (Saminu Alhassan)