Jaridar Daily Mail ta Zambia ta rawaito koci Simukonda na cewa nasarar da Zambia ta samu, na doke takwararta ta Cote d'Ivoire da ci 4 da 3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida ta dada karfafa masa gwiwa.
Duk da wannan tagomashi da kocin na Zambia ke ganin kungiyar sa na samu, a hannu guda ya ce dole ya kara karfin 'yan wasan gaban sa, gabanin sauran wasannin share fage da ake bugawa domin halartar gasar cin kofin gasar kulaflikan matasan wanda za a gudanar a kasar Senegal. Kuma kulaflikan da suka samu nasara a gasar za su wakilci nahiyar Afirka zuwa gasar Olympic ta birnin Rio a badi.
Kulaflikan da tuni suka cimma nasarar samun gurbi a gasar ta Senegal dake tafe sun hada da Algeria, da Masar, da Afirka ta Kudu da kuma mai masaukin gasar Senegal.
Bisa tsari kungiyoyi uku da suka samu zama a sahun gaba a gasar ta kasar Senegal, na da gurbin halartar gasar Olympic ta Rio kai tsaye, yayin da kuma kungiya ta 4 za ta fafata neman gurbin ta hanyar karawa da wata kasa daga nahiyar Asiya.(Saminu Alhassan)