A wasannin da aka buga a filin wasa dake Pointe-Noire, na kasar Congo Brazzaville
Congo 0 Nigeria 0, wanda hakan ke nuna Nigeria ta samu nasara kan Congo da tsiran maki, bayan da jimillar kwallayen wasannin da suka buga suka zamo 2-1.
A Blida na kasar Algeria kuwa, Sierra Leone 0 Algeria 0, kuma Algeria ta samu nasara ke nan da yawan kwallaye 2-0
Wasan da aka mayar birnin Bamako sakamakon barkewar cutar Ebola kuwa, Mali ta doke Gabon da ci da nema, don haka Mali ke kan gaba da yawan kwallaye 3-0.
Sai wasan birnin Lusaka, inda Zambia ta tashi wasanta da Ivory Coast babu ci bisa tazarar maki da Zambia ta samu na kwallo 4-3.
A Kampala kuwa, Masar ta doke Uganda da ci 2 da 1. Masar ta samu nasara da yawan kwallaye 6 da 1 ke nan.
Sai kuma wasan birnin Pietermaritzburg na Afirka ta tsakiya, inda Afirka ta Kudu ta samu nasara kan Zimbabwe da ci 3 da nema, kuma ta yi gaba da yawan kwallaye 4-1
A Rades na kasar Tunisia kuwa, Tunisia ta doke Morocco da ci 2 da nema. Don haka Tunisia ta shige gaba da yawan kwallaye 2 da 1.
Bisa jimillar wasannin da aka buga, kungiyoyi 7 da suka cimma nasara a wannan wasanni na share fage za su shiga gasar ta nahiyar Afirka da za a buga a kasar Senegal.(Saminu Alhassan)