Hukumomin Najeriya sun ceto mutane 281 daga tarkon masu fataucin bil adama a yankin kudu maso yammacin Lagos tsakanin watan Janairu da Yuli na wannan shekara, in ji wani jami'i a ranar Talata.
Joseph Famakin, kamandan cibiyar kasa dake hani da fataucin bil adama da makamantan haka ta (NAPTIP), wacce ta gabatar da wasu alkaluma ga manema labarai, ya bayyana cewa hukumarsa ta mayar da wasu mutane 252 da aka ceto daga hannun masu fataucin bil adama zuwa iyalansu bayan ta bude wani bincike da sanya ido kan iyalansu.
Dole ne NAPTIP ta tabbatar da cewa wadannan bayun Allah su koma cin hannun nagartattun mutane, domin kar irin wannan matsala ta sake faruwa, in ji mista Famakin.
Shugaban NAPTIP ya kara da cewa hukumarsa na da wata gidauniya da ke kula da irin wadannan mutane da aka ceto, domin ba su damar sake gina rayuwarsu.
Najeriya dai ta yi alkawarin yaki da ayyukan fataucin mutane tare da yin hadin gwiwa da gamayyar kasa da kasa, musamman ma kungiyoyin MDD da kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida. (Maman Ada)