in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta karbi shugabancin kwamitin sulhu na MDD na watan Augusta
2015-08-02 13:09:15 cri
Kasar Najeriya ta karbi shugabancin kwamitin sulhu na MDD na watan Augusta tun daga ranar Asabar.

Wakilin dindindin na Najeriya a zauren MDD, Uche Joy Ogwu ya karbi wannan mukami daga hannun takwaransa na kasar New-Zealand Gerard van Bohemen, wanda ya jagoranci kwamitin a cikin watan Juli.

Mista Joy zai shirya a ranar 4 ga watan Augusta wani taron menema labarai a cibiyar MDD dake birnin New York domin sanar da jadawalin aikin kwamitin. Kamar yadda kundin tsarin MDD ya tanada, babban wajibin kwamitin sulhu na MDD shi ne tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya.

Kwamitin sulhu na kunshe da mambobin dindindin biyar da suka hada da Sin, Amurka, Burtaniya, Faransa da Rasha, da kuma mambobin da ba na dindindin ba guda goma da ake zaben su bisa gungun mambobin biyar biyar sau daya a duk shekaru biyu.

Shugabancin kwamitin na kasancewa karba karba tsakanin mambobin kwamitin bisa aiki da jerin harufan Alphabe na sunan kasashe da harshen Turanci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China