Taron wanda aka bude a Talatar nan a birnin Khartoum, ya samu halartar karamin ministan ma'aikatar noma a kasar ta Sudan Yaqoub Mohamed Al-Tayeb, da jakadan Sin a kasar Li Lianhe, da kuma kwararru daga Sin da kuma wasu na kasashen nahiyar Afirka su 9.
Da yake tsokaci game da wannan batu, Al-Tayeb ya shaidawa mahalarta taron cewa Sudan na da burin amfani da sakamakon taron na wannan karo, wajen goyon bayan bunkasa sha'anin noma a nahiyar Afirka baki daya.
Shi kuwa a nasa bangare Mr. Li Lianhe cewa ya yi musayar dabaru tsakanin Sin da Afirka a fannin aikin gona da tsaron abinci, zai taimaka matuka wajen samar da daidaito da ci gaba a duniya.
Ana dai fatan taron na wannan karo zai baiwa mahalartan sa damar tattaunawa, da nufin habaka harkar noma a Afirka, ya kuma tallafawa hadin gwiwar Sin da nahiyar ta Afirka a wannan fanni.