A cikin sanarwar kwamitin ya jaddada cewa, bisa dokokin jin kai na duniya, kamata ya yi a girmama, a kuma ba da kariya ga 'yan jarida da ma'aikatan da ke da nasaba da yada labarai, masu aiki cikin hadari a yankunan dake fama da tashin hankula, irin kariyar da ake baiwa fararen hula.
Sanarwar ta kara da cewa kamata ya yi bangarori daban daban da rikicin ya shafa su sauke nauyin dake kansu game da kiyaye dokokin jin kai na duniya, ciki har da kiyaye tsaron fararen hula a yayin rikici.
Ban da wannan kuma, kwamitin ya yi tir da nuna karfin tuwo, da kisan gilla da suka faru a kasar Afirka ta tsakiya, wadanda suka haddasa hasarar rayuka da dama, da lalace gidaje. Kazalika an sake nanata goyon baya ga tawagar sojojin kasa da kasa dake kasar, wadda kungiyar AU ke jagoranta, da kuma rundunonin sojojin Faransa da Turai. Kana an yi kira ga sassa daban daban da su hada kai sosai tare da tawagar kasa da kasa.
Rahotanni dai sun tabbatar da harbe Camille Lepage, 'yar jaridar kasar Faransa mai shekaru 26 da haihuwa, yayin da take bakin aikin ta a kewayen birnin Bouar dake yammacin kasar Afirka ta tsakiya. (Bilkisu)