in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa ta bukaci MDD da ta gaggauta girke sojojin kiyaye zaman lafiya a CAR
2014-02-14 12:34:51 cri
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande, ya zanta da babban sakataren MDD Ban Ki-moon ta wayar tarho a jiya Alhamis 13 ga wata, inda suka tattauna kan yanayin da jamhuriyar kasar Afrika ta Tsakiya CAR ke ciki, har ma Hollande ya bukaci MDD da ta gaggauta girke sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar.

Bisa sanarwar da fadar shugaban kasar Faransan ta bayar, an ce, shugaba Hollande ya yi bayani yayin wannan zantawa cewa, dole ne kwamitin sulhu na MDD ya tabbatar da kudurorin da suka shafi wannan kasa, musamman batun hada kai da kawancen kasashen Afrika, don ganin an hanzarta aiwatar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasar.

Har illa yau, Hollande ya yi maraba da kokarin da Ban Ki-moon ya yi na jawo hankalin kasashen duniya, game da marawa kasar Afirka ta Tsakiyar baya. Rahotanni dai sun bayyana cewa, Hollande bai yi magana kan ko Faransa za ta kara girke sojoji a Afirka ta Tsakiyar ba.

Kafofin watsa labarun Faransa dai sun bayyana cewa, Ban Ki-moon ya taba kira ga Faransa, da ta yi la'akari da kara yawan sojojinta a kasar Afirka ta Tsakiyar, ko da yake kakakin ma'aikatar harkokin wajen Faransan Romain Nadal, ya bayyana a ranar 12 ga wata cewa, kasarsa ba za ta kara aika sojoji zuwa Afirka ta Tsakiyar ba. Ya ce, maimakon haka, Faransa na fatan sojojin MDD da na EU, za su tallafa wajen tabbatar da dawowar yanayin zaman lafiya da lumana a kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China