Babban kwamandan sojojin kasar ta Poland Leck Majewski, ya ce, shigar sojojin kasar ta Poland cikin aikin jin kai da zaman lafiya, ya bude wani sabon babi a dangantakar da ke tsakanin kasar Poland da Faransa.
Tawagar mai yawan dakaru 50, tana kunshe ne da dakaru 2-4 masu sarrafa jiragen yaki kirar Hercules C-130 da dakarun kasa da kuma jirgin saman dankon kaya kirar Hercules guda daya.
Bayanai na nuna cewa, daga Orleans na kasar ta Faransa, dakarun za su tashi zuwa Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta jirgin sama,inda za su yi aikin kare fararen hula, ciki har da 'yan gudnan hijira da ke samun mafaka a kusa da filin saukar jiragen sama, kuma za su kasance a can har zuwa karshen watan Afrilu.(Ibrahim)