Aikin fitar da albarkatun man fetur zai ci gaba nan da nan da zaran an samu gyara bututun da ya lalace, in ji Ibrahim Farinloye, kakakin Cibiyar kasa da ke kula matsalolin gaggawa NEMA, ta yankin kudu maso yammaci, a yayin wani taron manema labarai a birnin Lagos.
Wutar ta yi barna sosai a wannan yanki a tsawon kwanaki uku bayan fashewar bututun a ranar Litinin da yamma, lamarin da ake ganin ya da hannun masu satar mai.
Mista Farinloye ya bayyana cewa tun ranar Talata, ruwan sama da yanayin tabon kasa sun kawo cikas zuwa wannan wurin. Sai da aka kafa hanyoyi da katakai domin baiwa ma'aikata damar kai ga wurin, in ji wannan jami'i.
Mun kai ga wannan wurin da gobarar ta tashi, kuma tare da taimakon ma'aikatan dake kula da matsalolin gaggawa, aka samu kashe wutar. (Maman Ada)