in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanayin hakkin bil adama yana tsananta a CAR
2014-01-15 12:26:12 cri
Take hakkin bil Adama a kasar Afrika ta Tsakiya CAR yana kara tabarbarewa, in ji ofishin babban kwamishinan kula da hakkin bil adama, a ranar Talatan nan.

Rahoton binciken dake zuwa ofishin ya bayana cewa, take hakkin bil adama ya karu kwarai da gaske tare da fadar ramuwar gayya da suka hada da kisan kai, cin zarafi, gundule gabubban mutane da ba su ci ba ba su sha ba, tilasta wa mutane bacewa, wulakantar da mutane, fyade da kuma kai hari a kan mutane da gangan bisa ga akidar addininsu.

Rahoton ya zo ofishin ne bayan da ma'aikatan ofishin masu sa ido su 4 suka aiwatar da binciken jin ra'ayin mutane su 183 a wuraren da ake tashin hankali da suka hada da wadanda fadan ya rutsa da su da wadanda suka shaida hakan da idanunsu, da kuma sauran hanyoyin samun bayanai.

Yaduwar rashin bin doka da oda da take hakkin bil adama ya zama kan gaba a cikin bayanin da aka samu wanda ke bukatar daukan mataki cikin gaggawa, in ji Navi Pillay, babban kwamishinan ofishin kare hakkin bil adama na MDD cikin wata sanarwa.

A 'yan kwanakin nan, yanayin da ake ciki a kasar Afrika ta Tsakiya ya tsananta kwarai tare da take hakkin bil adama, duk da cewar an samu saukin tashin hankalin, an samu rahoton kashe wadansu mutane kusan 40 a babban birnin kasar Bangui kadai ranar Jumma'an nan da ta gabata.

An samu rahoton cewa, an gundule wadansu mutane gabubban su, wadansu kuma an sace su, sannan akwai bayanai dake nuna faruwar kwashe kayayyakin jama'a a fadin kasar, abin da ya sa Mr. Pillay ya yi gargadin cewar, duk da kokarin sulhu da ake yi a Bangui, wannan yanayin da ake ciki ya yi tsanani sosai, yana mai kira da a kawo dauki cikin gaggawa da zai dakatar da wannan aika aika. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China