Rahotanni sun bayyana cewa an yi awon gaba da Injiniyan ne tun a ranar Lahadi, kuma kawo yanzu wadanda suka sace shi ba su tuntubi kowa ba. Jami'an tsaro sun ce maharan sun sanya shinge a kan hanyar da Mr. Rody yake bi tare da direban sa, da sauran ma'aikatan jihar ta Naija su biyu ne a kauyen Ekila kan hanyar zuwa birnin Minna, sa'an nan suka tisa keyar mutanen bayan sun dakatar da motar da suke ciki.
Injiniyan wanda ke kan hanyar sa ta zuwa inda kamfanin Enerco da yake wa aiki ke gudanar da wasu gine-gine, na tare ne da sauran mutunen da aka ce ma'aikata ne na ma'aikatar ayyukan jihar Naija.
Wannan dai lamari ya auku ne a ranar da jami'an tsaron farin kayan kasar ke bayyana cewa, sun samu nasarar damke masu garkuwa da mutane su sama da 20 a sassan kasar daban daban. (Saminu Alhassan)