Najeriya: Jarirai dubu 250 suke mutuwa a kowace shekara sakamakon karancin kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya
A jimilce kimanin jarirai dubu 250 suke mutuwa a kowace shekara a kasar Najeriya dalilin karamacin kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya da kuma rashin ba da jinya mai kyau ga jarirai. Madam Elizabeth Disu mai ba da shawara ta bangaren kula da kananan yara a asibitin jami'ar jihar Lagos, ta shaida wa manema labarai a ranar Jumma'a cewa mutuwar jariri matsala ce da ake samu ko da yaushe duk da cewa Najeriya ta fi samun yawan mutuwar jarirai a nahiyar Afrika. A cewar madam Disu, talauci, karancin ilimi, rashin bada jinya mai kyau ga jarirai da kuma jinkirin da ake samu wajen zuwa asibitoci sun kasance muhimman abubuwan dake janyo mutuwar jarirai a wannan kasar dake yammacin nahiyar Afrika. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku