Wang Yi ya ce, duniyar da muke ciki ana zagaye ne da juna, kuma duk kasashen duniya suna da moriya iri daya. A kwanaki biyu da suka wuce, aka samu babban bala'in girgizar kasa da ba a taba irinsa ganinsa ba cikin shekaru 100 da suka gabata a Nepal, wadda kasa ce da ke makwabtaka da Sin, lamarin da ya jawo hasarar rayukar mutane da dukiyoyinsu. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Li Keqiang sun mika sakon ta'aziyya ga takwarorinsu na Nepal cikin lokaci, kuma kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa ta Sin ta isa wurin da bala'in ya shafa, kuma ta ceci wadanda suka tsira amma suka makale cikin buraguji da dama.
An kai kayayyakin da Sin ta tura karo na farko cikin gaggawa zuwa Nepal, wadda daya daga cikin kasashe marasa ci gaba a duniya, kuma ana bukatar agajin gaggawa daga kasashen duniya a Nepal, don haka gwamnatin Sin za ta yi iyakacin kokarinta don ba da agaji cikin gaggawa .(Bako)