A yau ne, aka kaddamar da taron tattaunawa karo na 11 a ma'aikatar harkokin wajen Sin,karkashin taken, "Leka lardin Hebei na Sin, don yin hadin gwiwar masana'antu tsakanin kasashen duniya, da samun moriyar juna". A jawabinsa wajen taron, ministan harkokin wajen na Sin ya ce, har kullum kasar a tsaye take don shiga cikin hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya a fannin masana'antu da sauran sana'o'i.
Yana mai cewa, dalilin da ya sa, Sin ta inganta hadin gwiwa da kasashen duniya a wannan fanni, shi ne don kokarta canja salon bunkasuwar tattalin arzikinta, da biyan bukatun kasashe masu tasowa. Hakan a cewar ministan, zai taimakawa kokarin kafa sabon nau'in dangantakar kasa da kasa ta hadin gwiwa da moriyar juna.(Bako)