Ban Ki-moon dake ziyarar aiki a kasar Norway, ya halarci taron koli na samun ci gaba ta hanyar ilmi na birnin Oslo. A yayin bikin bude wannan taro ne kuma ya bayyana cewa akwai bukatar dora muhimmanci ga bada ilmi ga mata, da ilmin da ake koyarwa a halin gaggawa. Sauran fannonin sun hada da na ilmi mai inganci, da zuba jari ga ilmi da dai sauransu. Ya ce idan har aka kai ga samun ci gaba a wadannan fannoni, hakan zai taimakawa matuka wajen ci gaban duniya cikin yanayi na walwala.
A daya hannun firaministan kasar Norway Erna Solberg, ya sanar a gun bikin bude taron, cewa domin sa kaimi ga kasashen duniya wajen zuba jari da kyautata tsarin taimakawa bada ilmi, kasashen Norway, da Chile, Indonesia da Malawi, da hukumar bada ilmi da kimiyya da al'adu ta MDD, sun kafa kwamitin taimakawa samar da damar bada ilmi na duniya, inda manzon musamman na MDD mai kula da harkokin bada ilmi, kuma tsohon firaministan kasar Britaniya Gordon Brown ya zama shugaban kwamitin. (Zainab)