A cikin kudurin da kwamitin mai mambobi 15 ya cimma, kwamitin ya kuma bukaci gwamnatin kasar Mali da kungioyin da ke dauke da makamai a cikin kasar da su cika alkawuran da suka dauka kana su mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wutar da suka cimma.
Kwamitin sulhun ya kuma dorawa tawagar MINUSMA da aka kafa a shekarar 2013 dake kasar ta Mali alhakin taimakawa shirin kasar na mayar da mulki ga hannun farar hula, da sa-idon ganin an aiwatar da yarjejeniyoyin tsagaita bude wuta da kuma na zaman lafiya da aka cimma a kasar.
Tun a watan Afrilu ne fada ya sake barkewa a arewacin kasar Mali tsakanin Buzaye 'yan tawaye da mayakan da ke goyon bayan gwamnati. MDD dai na kira ga bangarorin da ke fada da juna a kasar Mali da su kawo karshen matsalar da kasar ke fuskanta ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma. (Ibrahim)