A kwanan baya, kungiyar Greenpeace ta aika da wani sako ga wata hukumar gwamnatin Sin da abin ya shafa, inda ta bayyana cewa, wasu kamfanonin Sin sun yi karya kan yawan nauyin kayayyakin da jiragen ruwansu ke iya dauka a yayin da suke kama kifi a yankin teku dake kasashen yammacin duniya da sauransu.
Game da wannan batu, Hong Lei ya ce, gwamnatin Sin tana tsayawa tsayin daka kan bukatar kamfanonin kasar da su bi dokoki da daukar alhakinsu a yayin da suke yin cinikayya da sauran kasashen duniya, musamman ma kasashen nahiyar Afirka, a kokarin samun moriya ta hanya mai dacewa cikin adalci.
Hong ya ce, bisa labarin da aka bayar, an ce, wadannan jiragen ruwan sun gudanar da ayyukansu bisa amincewar gwamnatin Sin da kasashen dake mallakar wannan yankin teku, tare da samun izinin kama kifi da gwamnatin wadannan kasashen yammacin Afirka suka bayar.
A cikin 'yan shekarun da suka gabata, wasu kamfanonin Sin sun taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasashen da suke yin cinikayya da su, tare da ba da taimako a fannonin kara kudin haraji da kasashen ke samu, da sa kaimi ga samar da guraben ayyukan yi a kasashen, da kara yawan kudin shigar al'ummar kasashen da sauransu, da haka sun sami karbuwar gwamnatoci da jama'ar kasashen baki daya.(Fatima)