Shugaban kasar Kamaru Paul Biya da takwaransa na kasar Najeriya Muhammadu Buhari, da ke ziyarar aiki a kasar Kamaru, sun bayyana niyyarsu a ranar Laraba a yayin wata ganawarsu na yin aiki tare domin murkushe barazanar kungiyar Boko Haram ta Najeriya.
Kasashen Kamaru da Najeriya, sun kasance mambobi na gamayyar kasashen tafkin Chadi (CBLT) da ke kunshe da sauran kasashe kamar Chadi, Nijar da Libiya, da ke kokarin kafa wata rundunar hadin gwiwa domin yaki da Boko Haram.
Watanni hudu bayan zaben shi a matsayin shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya isa a safiyar Laraba a wata ziyarar aiki da abokantaka ta kwanaki biyu a birnin Yaounde, a cewar hukumomin kasar.
Ziyarar na maida hankali sosai kan yaki da Boko Haram, inda tun a shekarar 2013 ta fara kai hare-harenta zuwa kasar Kamaru, a shiyyar arewa mai nisa, hukumomin Yaounde dama suna dakon wannan ziyara ta shugaban Najeriya a kasar ta Kamaru.
Domin karrama bakon nasu, hukumomin Kamaru sun kebe babban tarbo inda aka kawata titunan babban birnin kasar tun daga filin jiragen saman kasa da kasa na Yaounde-Nsimalen har zuwa fadar shugaban shugaban kasar da manyan kyalaye dake dauke rubuce-rubucen da ke jaddada niyyar Yaounde na yin aiki tare da sabbin hukumomin Abuja, da ma kafa wata rundunar hadin gwiwa domin kawar da kungiyar Boko Haram.
"Ba za mu cigaba da barin wannan kungiya ta yadu ba. Dole mu hada karfi da karfe, da yin musanyar kwarewarmu", in ji shugaba Paul Biya a yayin wata liyafar da ya shiya wa bakonsa a ranar Laraba da yamma a fadar Unite, bayan tattaunawa ta awoyi biyu da rabi tare da takwaransa na Najeriya.
Tsakanin yin garkuwa da mutane da kashe al'ummomi, Boko Haram ta janyo fargaba, rashin tsaro, da tabarbarewar tattalin arziki da zamantakewar al'umma a Najeriya da ma zuwa kasashen Chadi, Nijar da Kamaru.
A 'yan kwanakin baya bayan nan, tsakanin ranar 12 zuwa 25 ga watan Juli, kimanin mutane kusan 60 suka mutu a cikin hare- haren kunar bakin wake biyar, inda uku a cikin kwanaki uku a Maroua, muhummin birnin kuryar arewacin Kamaru. (Maman Ada)