Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta yi nasarar ceto mutane 59 daga hannun mayakan Boko Haram, bayan wani samame da suka kaddamar a wasu kauyuka biyu da ke yankin Konduga a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Mataimakin kakakin rundunar sojojin Najeriya kanar Tukur Gusau ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua. Ya ce, mutanen da sojojin suka kwato sun hada da yara 25, da mata 29 da kuma tsofaffi maza guda 5.
Kakakin ya kuma bayyana cewa, sojojin sun yi nasarar kashe 'ya'yan kungiyar da dama a samamen na ranar Laraba, baya ga wata mota kirar Jeep da Tifa da aka kwato daga hannun mayakan.
Bugu da kari, sojojin sun lalata sansanonin mayakan da ke kashimbiri da kuma Warmure.
Daga bisani ne kuma ake sa ran damkawa hukumar agaji ta jihar Borno (SEMA) mutane da sojojin suka ceto domin a tsugunar da su.(Ibrahim)