Rundunar sojojin Najeriya da ke fafatawa da mayakan Boko Haram a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar ta bayyana cewa, ta kubutar da mutane 30 daga hannun mayakan na Boko Haram.
A wata sanarwa da mataimakin kakakin rundunar sojojin na Najeriya Kanar Tukur Gusau ya raba wa manema labarai, ya ce, daga cikin mutanen da dakarun suka yi nasarar kubutarwa a wani samame da suka kaddamar a garin Dikwa sun hada da yara 21 da mata 7 da kuma tsofaffi maza guda 2.
Kakakin ya ce, dakarun sun kuma gano wuraren koyon harbi da tukin jiragen saman yaki na 'ya'yan kungiyar a wasu wurare da aka lalata tare da kwashe kayayyaki a fadar Shehun Dikwa.
A makon da ya gabata ne dai sojojin na Najeriya suka kwato garin na Dikwa daga hannun mayakan na Boko Haram, bayan nasarar samamen da suka kaddamar a garin.
Mayakan na Boko Haram dai sun zafafa hare-haren kunar bakin waken da suka kaiwa da bama-bamai a sassan kasar, da kuma kasashen da ke makwabtaka da Najeriyar. (Ibrahim)