Dakarun Najeriya sun bayyana cewa, sun kama sama da dururruka da wasu gwangwanaye albarkatun man fetur sama da 4,000 da mayakan Boko Haram suka yi sumugansu ta kan iyakar Kamaru.
Kakakin mayakan sama na Najeriya Air Kwamado Dele Alonge wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafe ya ce, an gano wadannan kayayyaki ne a jerin matakan yaki da mayakan na Boko Haram da aka dauka.
A dai kama wadannan miyagun kayayyaki ne a kauyukan Pepe, Dashin-Hausa, Belel, Bilachi da kuma Konkul wadanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.
Kakakin ya kara da cewa, dakarunsu za su ci gaba da gano tare da lalata sansanoni da kafofin da mayakan ke samun makamai.
Bayanan sirri a Najeriya sun bayyana cewa, wannan nasara da mayakan kasar suka samu ta kassara harkokin mayakan na Boko Haram.(Ibrahim)