Fiye da mutane dari biyar aka killace domin sanya ido kan su, da ba su kulawa a yankin Tonkolili na kasar Saliyo, bayan an tabbatar da gano wani mutum guda da ya kamu da cutar Ebola a wannan wurin a makon da ya gabata.
Bullowar cutar ya sanya a aiwatar da matakin killace wani kauye baki daya, har zuwa tsawon kwanaki ishirin da daya, kana za a dauki matakan ladabtarwa kan maigarin kauyen, dalilin shirun da ya yi na rashin sanar da hukumomin kiwon lafiya, in ji Sidi Yayah Tunis, wani jami'in hulda da jama'a na cibiyar yaki da cutar Ebola ta kasar (NERC) a ranar Alhamis. Wannan matsala ta kawo karshen kwanaki 150 na babu wani wanda aka gano da ya kamu da cutar Ebola a Tonkolili. (Maman Ada)