150723-bastian-schweinsteiger-ya-koma-man-united-bello.m4a
|
Sai dai a ganin wasu manazarta harkokin wasanni, komawar Schweinsteiger kungiyar Man. United za ta iya haifar da illa ga wasu 'yan wasan kungiyar. Ganin cewa shigar wani sabon dan wasa na tilastawa a sauya tsarin kungiya, wanda hakan ke shafar rawar da wasu 'yan wasan ke takawa.
Ga misali Luke Shaw dake matsayin dan wasa baya bangaren hagu. Dan wasa ne mai shekaru 20 a duniya, yana kuma da karfin jiki sosai, wanda hakan ke ba shi damar kutsawa cikin abokan karawa. Sai dai ya kasa biyan bukatun babban kocin kungiyar ta Man. United Louis Van Gaal a fannin fasahar mika kwallo, daga gefen fili zuwa tsakiyarsa, gami da kokarin samun damar kai hari, lamarin da ya sanya tauraruwar dan wasan ta dishe, musamman ma ta la'akari da kasancewar Daley Blind, wanda ke da kwarewa sosai a matsayin dan wasan baya a gefen hagu, gami da Marcos Rojo wanda ya fi karfin wajen kai hari.
Shi kuwa Daley Blind, idan mun dubi yadda yake taka kwallo, za mu iya ganin kwarewarsa a fannin zabar lokacin kai farmaki gami da tsaron gida. Kwarewar sa a fannin lura da yanayin da kungiyar take ciki a ko da yaushe, ta sa dan wasan zama daya daga cikin 'yan wasan kungiyar Man. United wadanda suka fi yawan mika kwallo ga saura.
Bayan komawar Schweinsteiger Man. United kuma, kungiyar za ta samu 'yan wasan tsakiya 3 ke nan, wato shi kan sa Schweinsteiger, da Michael Carrick, da kuma Morgan Schneiderlin, don haka Blind ba ya bukatar buga tamaula a matsayin dan wasan tsakiya ke nan, kuma hakan ya sa ake sa ran ganin komawarsa tsaron baya a gefen hagu, wato zai maye gurbin Luke Shaw ke nan.
Ban da haka kuma, akwai Juan Mata wanda ake ganin cewa zuwan Schweinsteiger zai yi matukar tasiri ka makomar sa. Mata wanda dan wasa ne kwararre mai kuma fasahohi daban daban bai yi fice sosai ba, yana kuma rashin karfin jiki sosai, haka kuma ya kan yi "taka-tsantsan" yayin da yake bukatar ya mika kwallo. Don haka zuwan Schweinsteiger zai haifar kazamar takara tsakanin 'yan wasan tsakiya.
Har wa yau ganin yadda Mata ba shi da karfin jiki irin na Marouane Fellaini, da fasahar kai hari da tsaron gida ta Ander Herrera, gami da fasahar jagorantar sauran 'yan wasa ta Schweinsteiger, mai yiwuwa ne ya fita daga cikin ajin farko na 'yan wasan kungiyar.
Sa'an nan idan ba a manta ba, dalilan da suka sanya Schweinsteiger barin kulob din Bayern Munich, sun hada da kasancewar sa yana da fasahar taka leda irin ta Xabi Alonso, ta yadda ba abu ba ne mai yiwuwa su ci gaba da kasancewa tare su biyu a kungiyar. A daya bangaren kuma wannan matsala na iya sake bulla bayan zuwan sa Man. United, ganin yadda Schweinsteiger da Michael Carrick ke da kusan rawar irin daya a fannin taka leda.
Bisa matsayin 'yan wasan biyu na masu taka leda a tsakiyar fili don jagorantar kai hari, dukkansu na bukatar samun damar sarrafa kwallo, amma ko ta yaya za a raba wannan dama tsakanin su? Kuma wane ne zai kula da kai hari, yayin da dayan ke kula da tsaron gida? Tabbas dai daya daga cikin su ya yi rinjaye.
Manazarta ma na ganin kusan halayyar 'yan wasan daya ce, don haka ake ganin yiwuwar cin karo da matsaloli iri daya a fasahohinsu. Ga misali, Carrick ba shi da sauri wajen gudu, kuma baya iya sarrafa jikinsa cikin sauri, matsalolin da ake ganin irinsu shi ma Schweinsteiger ke da su. Don haka idan Van Gaal ya sanya dukkan 'yan wasan na sa biyu a tsakiyar fili, tabbas hakan zai zama batu mai janyo hankalin masu sha'awar wasan kwallon kafa, kuma ba zai taimaka ba wajen cin kwallo.
Idan kuma muka sake duba niyyar da Van Gaal ya dauka ta shigo da Schweinsteiger, za mu gano cewa wani yunkuri ne na karfafa fasahar sarrafa kwallo, da kuma kokarin daidaita tsohon tsarin kungiyar da Alex Ferguson ya bar masa gado.
Kamar yadda ake cewa kwallo fara da baka ce. Shigowar Schweinsteiger kungiyar Man. United mai yiwuwa ta haifar da matsi ga mutane da yawa, a daya hannun kuma ta yiwu hakan ya kauda matsalolin da kungiyar ta gamu da su a baya. A lokacin da kungiyar take neman sake farfadowa a teburin kulofilikan kwallon kafar kasa da kasa, abun lura shi ne duk wani dan wasa da ya shiga kungiyar, da duk wata sabuwar fasahar da za a dauka, ko duk wata nasarar da kungiyar ta cimma, za su tabbatar da makomar kungiyar a nan gaba. (Bello Wang)