in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta tallafawa Afirka a fannin yaki da ta'addanci da yaduwar cutar Ebola, in ji Ban Ki-Moon
2015-01-31 16:28:16 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya ce Afirka za ta ci gaba da samun goyon baya da tallafin MDD, a fannin yaki da ayyukan ta'addanci, da dakile yaduwar cutar Ebola.

Mr. Ban wanda ya bayyana hakan cikin jawabinsa ga mahalarta taron kungiyar AU karo 24 a jiya Jumma'a, ya ce ta'addanci da cutar Ebola, sun zamewa Afirka annoba, dake haifar da koma baya ga ci gaban nahiyar baki daya.

Kaza lika Ban ya bayyana matukar takaicin yadda hare-hare masu tsattsauran ra'ayi, ke janyo salwantar rayukan fararen hula a kasashen Afirka, kamar Kenya da Najeriya da Mali da Libiya da Nijar.

Daga nan sai ya yi kira ga shugabannin kasashen nahiyar da su hada karfi waje guda, domin ganin bayan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Ya ce MDD za ta ci gaba da hadin gwiwa da hukumomin nahiyar, a kokarin da ake yi na dawo da kyakkywan yanayin tsaro, da ci gaban nahiyar.

Babban magatakardar MDDr ya kara da cewa, MDD na da burin tallafawa Afirka, wajen warware matsalolin siyasa, da tashe-tashen hankula, dake addabar kasashe irin su Somaliya, da Sudan ta Kudu, da Afirka ta tsakiya, da kuma Libiya.

Har wa yau Ban ya yi kira ga kasashen duniya da su kara tallafawa, a fannin yaki da cutar Ebola.

Ana dai sa ran yayin taron AUn na wannan karo, shugabannin Afirkan za su tattauna, game da yiwuwar tura dakarun hadin giwa na musamman, domin fatattakar mayakan Boko Haram a arewacin Najeriya. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China