Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, yawan jarin da kasashe masu tasowa suka saka a wannan fanni ya karu da kashi 36 cikin 100 a shekarar 2014, har yawan jarin ya kai dalar Amurka biliyan 131.3, inda kasar Sin ta kai matsayin farko a duniya bisa yawan jarinta da ya kai dalar Amurka biliyan 83.3, yayin da kasashen Brazil, da India, da Afrika ta Kudu su ma ke cikin jerin kasashe 10 na farko a duniya. A sa'i daya kuma, yawan jarin da sauran kasashe masu wadata suka saka a wannan fanni ya karu da kashi 3 cikin 100 kacal.
A cewar Mr. Steine, yawan wannan nau'in makamashi ya zama wani muhimmin kashi wajen raya makamashi, da muhimman ababen more rayuwa a kasashe masu tasowa. Makamashi da ake sake amfani da shi na taka muhimmiyar rawa wajen canja salon tattalin arziki na kasashen