A yau da dare ne kuma ake saran mambobin kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya 85 za su jefa kuri'u don zaben birnin da zai karbi bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi ta hoton bidiyo, inda ya nuna goyon bayansa ga birnin na neman shirya gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi. Ya ce, jama'ar Sin na fatan samun wannan dama,kuma idan har aka zabi birnin Beijing, tabbas Sin za ta shirya gasar wasannin Olympic mai kayatarwa kuma cikin nasara.
Mataimakiyar firaministan kasar Sin Madam Liu Yandong ta ce, gwamnatin Sin a shirya ta ke ta kebe isassaun kudade da matakan tsaro don shirya gasar wasannin na Olympics.(Bako)